LITTAFI: DANGARTAKAR ZUCI.

AN

BISSMILLAHIR RAHMANUR RAHIM

Dukkan godia sun tabbatar ga Allah (SWA), da ya bamu ikon rubuta wannan littafin, tsira da amincin Allah su k'ara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), Yah Allah yanda ka nufe mu da fara rubuta wannan littafin Allah ka bamu ikon kammala shi lafiya
Wannan labarin littafin bamu yi shi don wani ko wata ba kirkirarren labari ne dafatan masu karatu xaku biyo mu don jin kalar wannan labarin na *DANGARTAKAR ZUCI*

     Wata er yarinya ce kyakkyawa irin  chocolate colour nan tana sanye da wata er farar vest irin ta yara da yake lokacin xafi ne sai k'aramin wandon vest d'in farare ne sol kalar su sai dai kuma kash duk sunyi datti kayan sosai duk sun fita hayyacin su ita ma tayi dukun dukun gaba d'ayan ta, er kimanin 7year's tana 6uruntu a kitchen duk da tsayin ta bai kai ba sai da ta taka kujera tukunna ta bud'e wata tukunyar miya tasha naman kaji xuk'u xuk'u a ciki wani babban spoon da plate ta d'auko ta tsomashi acikin miyar sai da ta kwashe naman ciki Kaf gaba d'aya sannan ta mayar ta rufe tukunyar tare da sakko wa daga kan kujerar.

   A k'asa ta xauna ta hau cin naman nan hannu baka hannu kwarya tana sauri don kada a shigo a gan ta a haka, tayi nisa acikin ci sosai don ta kusan cinye rabin naman sai ga wata er dattijuwa ta shigo kitchen d'in tana ganin ta sai ta buga salati tare da cewa
" Husna!!! "
Da sauri yarinyar da aka kirawo da husna ta d'ago kanta tuni ta kwa6e baki xata sau kuka cikin sauri er dattijuwar nan kakar su suna kiranta da hajia maamaa taxo ta fisge plate di'n hannun husna cikin fad'a ta fara cewa
"yanxu fisabillah husna kin kyauta ki kwashe dukka naman abincin kisa a gaba Kina ci sai kace naki ne ke kad'ai, yarinya kamar mayya Indai taga nama sai taci "
Tuni husna ta 6are baki ta fara kuka sosai har da majina tana kok'arin xubo wa hararar ta hajia maamaa tayi tace
"bari yayan ku ya shigo Kinsan baya cin abinci sai da nama koh, gashi kin ta6a wannan baci xai yi ba wallahi ke dashi ba ruwa na, ja'irar yarinya fita daga kitchen d'in nan kije babar ki tayi miki wanka ji yanda kika xama yarinya sai shegiyar kaxanta "

Da gudu ta fice daga kitchen d'in tana rusa kuka har da d'ora hannu akai, girgixa kai hajia maamaa tayi tare da rufe plate di'n naman nan tana cewa
"Bari su na'ima su shigo sa ci don nasan ko Karen hauka ya ciji yayan ku baxai ci naman nan ba"

A parlour ta tarar da husna mai kuka har ta 6ingire da bacci hannu a baki ga hawaye sun bushe a fuska banda majinar hancin ta da ta bushe ita ma sai faman ajiyar xuciya take, girgixa kai ta sake yi a karo na biyu tare da ta6e baki tace
"ohhh ni ma'u yanxu ja'irar yarinyar nan bata tafi Anyi mata wankan ba sai taxo tana yi min bacci a parlour "
D'an tsaki taja tare da xama kan kujera ta d'auke glass d'in ta ta kwama a fuska tana kallon tashar sunnah T.v  sun sako wa'azin sheik Isah Ali pantami ta nutsu tana sauraren wa'azin.

Acikin nutsuwa ya shigo parlourn da sallama hajia maamaa ta amsa mishi sallamar tashi cikin matuk'ar gajiya da wata uwar yunwa da yake ji ya nufi kitchen bai kula ta ba kamar 2 seconds ya fito daga kitchen d'in a fusace ya Kalli hajia maamaa da take xaman jiran abin da xai ce yace
"maamaa uban waye ya cinye naman miyar nan? "
Kai tsaye hajia maamaa tace
"wa kasan xai cinye Idan ba ja'irar yarinyar nan ba husnah ita na kama a kitchen tana ci"
"kenan da kanta ta d'iba "
"k'warai da gaske"

Ya bud'e baki xai sake magana idon shi ya sauka kan husnah wadda take bacci hankali kwance a xuciye ya K'arasa inda take bai yi wata wata ba yasa hannu ya falla mata mari a gigice ta mik'e tana xunduma ihu hannun ta dafe da kumatun ta
"keeee kaxama rufe min baki yau sai jikin ki ya fad'a miki"
Belt d'in jikin shi ya fara kok'arin cirewa tuni ta hau rarraba ido jikin ta sai faman 6ari yake saboda tsabar tsorata don tasan halin Yah ibraheem akwai mugunta

Bata ankara ba taji saukar duka ta ko'ina tuni ta fara xunduma ihun axaba, hajia maamaa kuwa ko kallon Inda suke bata yi ba K'arshe ma sai ta shige bedroom don ita ta ja, shi kuwa ibraheem ya d'aga belt d'in ya xuba mata ta biyu Kafin ya ankara sai ga fitsari ajikin kafar shi husnah ta saki Haba ae tuni ya dad'a fusata yasa kafa ya haure ta ta fad'i k'asa tare da buga kanta jikin glass table da yake tsakiyar Parlourn ae kuwa ta k'walla wata raxannaniyar k'ara

Mtswww yaja wani uban tsaki a dai dai Lokacin wani guy ya shigo parlourn da sauri duk ya rud'e ya nufi inda take ya d'ago ta xuwa jikin shi bai damu da dattin jikin ta ba adai dai lokacin hajia maamaa ta fito daga bedroom d'in don ta kasa xama jin kukan husnah yayi yawa kada ibraheem yaji mata ciwo...........

 Kallon kafar shi da k'asan wandon shi yayi yanda suka jik'e da fitsari kamar xai fashe da kuka haka yake ji xuciyar sai tafasa take ya fara cire dogon wandon trouser di'n da yake jikin shi cikin k'ank'ami Ya yar dashi daga shi sai T-shirt da boxer kawai ajikin shi, suna had'a ido da Yah Abdullah ya sakar mishi harara tare da cewa
"ibraheem me tayi maka kayi mata wannan uban dukan haka? "
D'an ta6e baki yayi Kafin yace
"ka tambayi maamaa xata baka labari "
Yana gama fad'in hka ya fice daga parlourn,sai da yaje d'akin shi yayi wanka sannan ya shirya ya fito direct part d'in mamee yayi da sallama ya shiga aka amsa mishi ko'ina fes sai tashin k'amshi yake a rayuwar ibraheem ya tsani kaxanta baya shiri da kaxamai ko Kad'an xube wa yayi kan kujera ya Kalli mamee yace
"mamee I'm very hungry and tired "
Cikin kulawa mamee tace
"Ohh sorry my boy, bari na xuba maka abincin"
Tana gama fad'in hka ta shiga kitchen da sauri ta xubo mishi fried rice nd costlow sannan pepper chicken sai wani hadadden kunun aya ta kawo mishi cikin sauri ya bud'e plate di'n wani k'amshi ya doki hancin sa ya lumshe ido tare da sakin wani lallausan murmishi yace
"wow that's my favorite food thank u mamee nah"
Murmishi mamee tayi kawai nan ya fara cin abincin cike da jin dad'i ko five Spoon's bai yi ba aka bud'e kofar parlourn aka shigo xumbur ya mik'e tsaye tuni fuskar shi ta rine da 6acin rai tsantsa kallon ta yake kamar xai yi amai cikin tsawa yace
"hey u uban waya kawo ki nan kuma, (Ohh kuji ibraheem da k'arfin hali part d'in su ne fah) "
Cikin mamaki Yah Abdullah yace
"gidan nasu kace uban waya kawo ta to nine "
6ata rai yayi sosai yana wani kau da fuska mamee dai ko kallon su bata yi ba Idan da sabo ta saba da ganin wannan tsakanin ibraheem da husnah don hka news paper d'in dake kan table ta dauka tana karanta wa

Kamar ance ibraheem jiyo ka Kalli husnah yana kallon ta yaga wata majina ta fito ta hancin nata zuuut ta xuk'e ta wato ta shanye ta sai faman rarraba ido take wayyo Allah tuni ibraheem ya fara kakarin amai da gudu ya fice daga parlourn yana rik'e da ciki da baki, haushi ne ya ishe Yah Abdullah yace
"wallahi sai na saita wa ibraheem kai wannan iskancin nashi ya isheni wlh"
"a'a ba ruwan ka dashi wlh ae da gaskiar shi ji yanda jikin yarinyar nan ya koma don Allah waxai so ta tsaya a gaban shi yana cin abinci "
Girgixa kai kawai Yah Abdullah yayi tare da cewa
"toh mamee don Allah kiyi mata wanka lokacin islamia ya kusa"
"toh Shikenan "
Tashi tayi tare da kama hannun husnah suka nufi bedroom don yi mata wanka, yayin da Yah Abdullah ya fice daga part d'in.

Wanka sosai mamee tayi mata tare da wanke dogon gashin kanta irin na fulanin asali a gurguje ta shirya ta cikin uniform d'in islamia ta fito caras kamar ba husnar d'axu ba, da kanshi Yah Abdullah ya kai su islamia tare da sauran en uwanta.........
                                     
*TUSHEN LABARI*

  Alhj ibraheem da hajia Asma'u en asalin garin adamawa ne fulanine na usuli aiki ne ya dawo dashi garin kaduna d'an boko ne na bugawa a jarida, sun haifi yara 4, muktar, mustapha,umar, sai autar su fatyma sun bawa yaran su ilimi na addini dana boko sun taso cikin tarbiyya mai kyau ga nutsuwa suna matuk'ar kaunar junan su sosai.

Gida babba Alhj ibraheem ya gina yayi part 4, kowanne part yana da girma kuma k'asa da sama ne ya bawa 'ya'yan shi maxa uku kowanne part d'aya idan sunyi aure sai su xauna saboda su fi xumunci da juna da kuma shakuwa, shi kuma ya xauna a nasu part d'in na cikon na hud'u sai dai su nasu flate ne babu bene kuma yana tsakiyar na 'ya'yan nashi.

Alhj muktar yayi aure da matar shi hajia halima suna kiran ta da mumy, suna da yara har guda 5, Abdullah, ibraheem wanda yaci sunan kakan su sai khadijah, Amina, Fadila ce K'aramar su.

Sai Alhj mustapha da matar shi hajia zulaihat suna da yara 5, kabeer, mus'ab, ummu aimana, marwa da autar su habiba wadda taci sunan babar Alhj ibraheem suna kiranta da Ilham.

Da kuma Alhj umar da matar shi hajia zuhra da yaran su 3, yaseer,rufaida da Asma'ul husna mai sunan hajia maamaa suna kiranta da husna, sai autar su fatyma tana auren wani babban d'an kasuwa itace matar shi ta biyu tana da yara 2 mata sai namiji d'aya, farida, raudah sai bilal, wannan familyn suna xaune lafia da kwanciyar hankali ga had'in kai da xumunci hka matan ma suna xaune lafia xamane na wayayyu kowanne da aikin shi .

Dukkanin su kyawawa ne kunsan Fulani akwai kyau masha Allah gasu farare ne sol gaba d'ayan su Idan ka d'auke husna da chocolate colour wato mai duhu bata kaisu haske ba amman duk tafi so kyau gashi kamar su d'aya da ka gansu ka ga en uwan juna, don Alhj ibraheem da hajia Asma'u auren xumunci akayi musu.

Duk gidan nan ibraheem IB jinin su bai hadu da husna ba ya tsane ta dalilin tsanar kuwa irin husna kaxaman yaran nan ne duk kuwa da tsabtar mameen ta kuwa brush bata cika yin shi kullum ba sai mamee ta danneta tayi mata shi ta dole tana kuka da ihu sannan haka ma wanka don hka shi yasa ko abu ta ta6a ibraheem baya ta6a shi balle yayi amfani dashi da ace duka yana sa tayi tsabta da tuni husna tayi ko karatu Bata mayar da hankali akan shi sai wasa kawai, ga shegen cin naman tsiya kamar mayya ko a abinci ta gani ta kwashe ta cinye shi.

Shi kuwa Yah Abdullah duk acikin yayan ninsu yafi bata kulawa fiye da kowa shi yake lalla6a ta daga shi sai mumyn su ibraheem suna sonta sosai.
Ibraheem yasha siyan abubuwa ya raba wa kanannen shi Amman ban da husna haka xata k'ara ci kukan ta baxai Bata ba sai dai idan Yah Abdullah yana nan ko Mumy sai su bata, kuma ba ruwan shi Ko agaban mameen ta kuwa xai ci xalinta baya kiran sunan ta sai kaxama ko mummuna baka kinfa kowa muni a gidan nan ko abu baya ci Idan husna tana wajen saboda tsabar k'amk'amin ta.

Hajia maamaa tana bala'in son ibraheem duk cikin jikokinta tafi son shi, shima yana sonta sosai shi yasa ya dawo part d'in ta da xama gaba d'aya ,Hka kusan sauran yaran ko dayaushe suna part d'in ta.

Yah Abdullah yana karantar account ne a jami'ar ABU dake cikin garin xaria yayin da ibraheem yake karantar physiology shima a ABU di'n sai dai Abdullah yana gaba dashi, IB ya had'u ta ko'ina tun yanxu emmata suna kawo mishi rububi, miskiline na k'in k'arawa ga jan aji yana kuma da kamun kai ba ruwan shi da irin shiriritar nan na matasa yana da dad'in xama Idan har ka fuskan ce shi.

Ibraheem muktar ibraheem kyakkyawa ne fari ne sol dashi gashi dogo tubarkallah yana da hanci ga manyan idanu sajen shi da ya kwanta akan kyakkyawar fuskar shi ba k'aramin k'ara fito mishi da kyan shi yayi ba gashin kanshi kuwa irin na fulanin asali ne mai laushi da santsi kai ta ko'ina IB ya had'u
Acikin xuciyar Ibraheem IB yana da wani buri a xuciyar shi wanda shi da
*DANGARTAKAR ZUCIyar*
shi ne kad'ai suka san tsawon lokacin da yake cikin xuciyar shi yak'i bayyana shi ga kowa yana jiran lokaci da ya kamata ya bayyana shi...............
"Yau ta kama saturday, gaba daya jikokin hajia maamaa suna xaune a babban palour d'inta,ko wannen su dauke da littafi a hannunsu yayyan su na masu lesson. Ibrahim xaune a gefen maamaa suna hira da ita, a hankali husna ta bankad'o curtain d'in d'akin tana hangawa, gaba d'aya ta tsure,ibrahim na daria hankalinsa ya koma bakin kofar, ganin husna na rabe rabe yasa ya saki wani murmushin mugunta, bata rai yyi ya kalleta, cikin tsawa ya kirata, xonan husna.

"Sanye take da wata multi colour gown iya gwiwarta, gashin kanta daure da blue ribbon sai sheki yake, school bag ce rataye  a bayanta, sai kwalin exotic da ta taho dashi tana sha. Yau kam husna fes take dan ynx mamee ta gama mata wanka sannan ta kad'o kanta.

"Gaba d'aya hankalinsu yyi wajen ganin husna yasa wasu suka fara tausaya mata, dan bbu sauki tunda ya abdallah baya nan,dama shi kad'ai ne xai iya dakatar da ibrahim.

"Jiki na bari ta karaso cikin palour harta fara kuka, gaba daya jikinta bari yake dan a dunia tana bala'in tsoron ibrahim, a hankali ta tako kusa dashi ta tsugunna k'asa, ya ibrahim gani ta fada tana rawar murya.

"Hannun yasa ya kama kunnen husna ya rike, cikin karkausar murya ya fara magana, husna dan ubanki mai ya hanaki xuwa lesson tunda xu? Yarfe hannu take dan kunnenta xafi yake mata. Ya ibrahim har xan taho mamee na ta hanani wai sai ta mini wanka dan Allah kayi hakuri, wani wicked smile ibrahim yyi ya kalli husna, oya tashi ki mini jump frog, ido husna ta fito dashi hawayen fuskarta na xuba, dan ita tunda take bata taba yin jump frog ba.

"Ya ibrahim...... Bata karasa ba ibrahim ya dauke fuskarta da mari, a kasa husna ta xube tana kuka, tsawa ya daka mata ki tashi nace kiyi jump frog.
"Gaba daya maamaa ta tsure dan batasan ganin yarda ibrahim yake dukan husna kamar jaka, amma bbu damar magana dan bata kaunar bacin ransa. Kabeer da mus'ab ne suka tashi a fusace suka bar palour dan baxasu iya ganin wannan xalincin ba, gashi bbu damar magana tunda duk palour din ya girmesu, and a kwai respect a tsakanin su.

"Su khadija, amina, fadila, ummu aimana, marwa, habiba, sai rufaida yayar husna. Gaba dayan su kuka suke a boye dan kar ya ibrahim ya gani suma ya saka su jump frog din. A hankali husna ta tashi fuskarta shabe-shabe da hawaye da majina, cire school bag din ta tayi ta ajiye a gefe ta fara jump frog.

"Motar abdallah ce ta danno cikin gidan, tafe yake yana nishadi, ganin Kabeer da mus'ab yyi sun fito a fusace daga part din maamaa yasa hankalinsa ya tashi, tabbas yasan akwai abinda ke faruwa, wani birki ya ci a gabansu bai kashe motar ba ya fito ya na tambayar su ko lpy? Cikin bacin rai kabeer ya bawa abdallah labarin abinda ke faruwa, bai bari sun kai karshe ba ya nufi part din maamaa da gudu.

"Ba tare da sallama ba ko kuma tuna cewa ana sallama, abdallah ya bankad'o curtain din palour yana huci kamar xaki, husna ya gani baiwar Allah ta dage tana jump frog kafafunta har sun mata nauyi "Ibrahim! Abdallah ya kira sunan sa rai a bace, jin muryar ya abdallah yasa husna taji wani sanyin dadi dan tasan" karshen wahalarta" yaxo, sunan novel din sister, xubewa tayi a wajen tana maida numfashi dan kuka ya gagareta.
"Cikin xafin nama ya abdallah ya dauke fuskar ibrahim da mari, dafe wajen ibrahim yyi idonsa a kan husna da ya tabbatar akanta ya abdallah ya mareshi, wata tsanar ta yaji ta kuma lunkuwa a ransa.                         
"Salati maamaa ta dauka tana tafa hannu, abdallah ibrahim din ka mara? Ta fada tana duba inda ibrahim ya dafe,.        "Abdallah ji yyi wani bakin ciki ya cika masa xucia, dan tunda ya shigo baima san da xamanta a palour din ba, duk da yasan ko tana nan ba magana xatayi ba.

" Kallon ta yyi cike da bacin rai, au maamaa da kina xaune? Kallon abdallah tayi da ina ina kake tunani ta fada rai a bace. Gaskia wannan bayi bane kuma bai dace ba, yama xa'ai ibrahim yasa husna jump frog a gabanki macace fa ba namiji ba ballantana kice.

"Baki maamaa ta saki au abdallah rashin kunya xaka mini? To wallahi bari babanka ya dawo xaixo ya sameni, xan basa labarin duk abinda ka mini, kuma mai kake nufi? Yarinya sai tayi laifi a gyaleta kenan.Tsaki taja ta cigaba da duba fuskar ibrahim.

"Sauran yaran kam a hankali suka fice dan indai ya abdallah ya fita ibrahim kansu xai dawo.

"Abdallah ne ya dauki husna gaba daya tausayinta ya cika masa xucia, cikin xafin nama ya fita daga palourn. Rasa inda xai kai husna yyi dan yasan idan ya kaita wajen mamee d'inta kamar cin fuska ne, dan matar nada hkr, tana bala'in dauke kai a kan cin kashin da ibrahim keyi wa husna.
"Part din hajia halima, wato momyn su abdallah ya nufa, da sallama ya shiga, sa'a yyi momy na palour dan haka tana ganin sa da husna ranga ranga ta mike ta nufi abdallah tana tambayar sa ko lpy? Cikin bacin rai abdallah ya bata labari. Momy ma kam ibrahim ya fara kaita bango, duk da tasan irin haka na faruwa idan jininka bai xo daya dana mutun ba amma abin ibrahim ya gawurta.

"Husna kam ta lafe a jikin ya abdallah tana sauke a jiyar xucia, momy ce ta karbeta ta kwantar da ita a kujera, mai aikin gidan ta kira ta kawo mata ruwan xafi da towel, sosai ta gasawa husna kafarta tana kuka dan kafar ta mata tsami.

"Ib na xaune a part din hajia maamaa gaba daya ta wani yi kicin kicin akan marin da abdallah yyi wa ibrahim, shi kuwa ibrahim a bangaren sa tunda husna ta sa a kanta aka mareshi to tabbas ynx ya fara axabtar da ita xai ga wanda xai hanashi.
    Bayan Mumy ta gama gasa mata kafar ne wani wahalalen bacci yayi awon gaba da husna sai faman sauke ajiyar xuciya take, mumy da Yah Abdullah sun xuba mata ido cike da tsananin tausayin ta a hankali Yah Abdullah ya sauke numfashi tare da cewa
"a gaskiya mumy ya kamata kiyi wa ibraheem magana akan abin da yake yiwa husna"

"ni fah wlh har kunyar mamee nake akan abin da yake mata, kuma ko a fuskar ta bata nuna rashin jin dad'in abin da yake ma husna, yanxu ace kana ganin da ace wata mara hak'urin ce ae da tuni ana tafka rigima don ba kowacce uwa ce xata juri hakan ba"

Mumy ta fad'i fuskar ta d'auke da tarin damuwa, Yah Abdullah ne ya cigaba da cewa
"wlh kuwa mumy ae mamee tana da hak'uri tana kallo yana yiwa husna mugunta amman ji yanda take bala'in son shi komai ta samu ibraheem ji fah ko wannan week d'in da ta d'auki salary di'n ta rabi ta bashi wai ya dunga xuba mai a mota (da yake mamee likita ce tana aikin ta) "
Yah Abdullah ya K'arasa fad'i cike da takaicin abin da ibraheem yake,
"shi yasa wlh nake son ta, amman xan mishi magana naja mishi kunne ba ruwan shi da ita"

"Yawwa mumy Allah yasa yaji, don hajia maamaa ce take goya mishi baya komai yace Shikenan ta hau kai ta xauna "

"Hmmm Allah ya kyauta "
"Ameeen "
Yana fad'in hka ya fice daga falon mumy ya nufi part d'in su na maxa, d'akin shi ya shige tare da xube wa kan gado xuciyar shi ba dad'i da abin da IB yake da Hka bacci ya d'auke shi.
Karfe 1 na rana school bus d'in su husna ta shigo cikin gidan tayi parking a hankali suka fara fito wa daga motar, da yake husna Fadila, Ilham da raudah (d'iyar kanwar su Alhj muktar ta dawo gidan da xama saboda duk kusan sa'annine dasu husna, shi yasa ta gudo gidan da xama tafi jin dad'i Idan tana cikin su), dukkanin su class d'aya suke a school .

A matuk'ar gajiye husna ta sakko daga motar yunwa ce take nukurkusar ta gaba d'aya sun riga ta shige wa cikin gidan saboda yanda take tafiya a hankali.

Tun daga nesa ya hango ta wani murmishin mugunta ya saki don yau kusan k'wana 2 basa had'u wa, sam bata kula dashi ba saboda hankalin ta yayi gaba sai ji tayi yace

"keeee er bak'a xo nan "
Wayyo Allah kamar husna ta d'ora hannu akai ta saki ihu haka take ji don tasan yau kam ta shiga dubu ba uku ba, saboda tsabar rud'ewa ta kasa K'arasa wa inda yake sai da ya sake daka mata tsawa sannan ta nufi inda yake jikin ta yana 6ari.

Kneel down tayi a gaban shi sai da ya d'auki tsawon mintuna 5 yana kallon ta kafin ya kau da kanshi cikin yatsine fuska yace

Ku biyo mu don cigaban littafin
Reactions

Post a Comment

0 Comments