DA DUMI-DUMINSA: Bishop Mathew Kuka ya yi kira da a gaggauta kamo wadanda su ka kashe tare da kona budurwar a Sokoto

Bishop Mathew Kuka ya yi kira da a gaggauta kamo wadanda su ka kashe tare da kona budurwar da ta yi batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.w 


Babban malamin addinin Kiristanci a jihar Sokoto Bishop Mathew Kuka ya yi kira da a gaggauta kamo wadanda su ka kashe tare da kona budurwar da ta yi batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.w a yau Alhamis a makarantar Shehu Shagari College.

Mathew ya ce tsawon shekaru suna zaune da musulmai lafiya a jihar Sokoto, don haka suna bukatar hukuma ta gaggauta kamo wadanda su ka aikata wannan kisan.

Daga karshe Mathew Kuka ya yi kira ga Kiristoci a jihar Sokoto da su kwantar da hankalin su.


Ana shi jawabin da ya fitar, Mai girma Sarkin Musulmai Alh. Sa'ad Abubakar, yayi Allah wadai da faruwar wannan.

Ya kuma bukaci jami'an tsaro da su yi bincike don kama wadan da sukayi wannan danyen aiki na daukar doka a hannunsu.

A yanzu haka dai an kulle Kwalejin Shehu Shagari dake Sokoto saksmakon faruwar wannan Abu.

Reactions

Post a Comment

0 Comments